Kasuwar 'Yan Fata, Maiduguri

Shirin Kasuwa a wannan makon ya kai ziyara 'Yan Fata, kasuwar da ake hada-hadar fatu a garin Maiduguri da ke jihar Borno, inda 'yan kasuwar suka koka akan yadda kalubalen tsaro ya shafi harkokin fatu.

Sana'ar fata na daya daga cikin tsofaffin sana'o'in da ke gudana a kasashen Afrika da yawa shekara da shekaru. 'Yan kasuwar fata na tsallakawa wasu kasashen Afrika su sayo fatun don sarrafasu ta hanyoyi dabam-daban, wani lokaci kuma a kai su wasu jihohin don sarrafa su a matsayin nama da eke kira Pomo, musamman a kudu maso yammacin Najeriya.

Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, na daya ga cikin jihohin da aka kafa irin wannan kasuwa ta hada-hadar fatu fiye da shekaru 100 da suka gabata, sai dai lamarin rashin tsaro a yankin ya shafi wannan sana'ar.

Saurari cikakken shirin daga Haruna Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Kasuwar 'Yan Fata, Maiduguri