Kasuwar Kan Iyakar Najeriya Da Nijar Ta Shiga Matsalar Rashin Takardar Naira

Sabbin kudin Naira

Karanci da rashin sabbin kudaden naira na haddasa rudami a kasuwar kan iyakar Najeriya da Nijar
Rikita rikitar canjin Naira a Tarrayar Najeriya na rutsawa da kasuwar kasa da kasa ta Illela, Jahar Sokoto, da ke karbar masu cin kasuwar a kowane karshen mako daga kasashen yammacin Nahiyar Afrika kamar Nijer, Benin, Mali da sauran su.
Abin da ya tilasta 'yan kasuwar wannan iyakar amfani da kudaden jamhuriyar Nijar, sai dai wadansu daga cikin 'yan canji da ma yan kasuwar sun koma karin kudin ruwa a wurin kasuwancin, abin da ke iya zama wani bala'i ga al'umma.w
Wannan kasuwa ta kasa da kasa ta karamar hukumar mulkin Illela a cikin jahar Sokoto mai iyaka da jamhuriyar Nijar da yan kasashen Nijar, Benin, Mali, burkina Faso da sauransu ke ci a kowane mako, ta shiga tsaka mai wuya sanadiyyar canjin kudaden Naira na Najeriya.
A yanzu haka, kudaden Najer a ke amsa a kasuwar ko ka koma kasar ka hannu sake.

Shin minene ya kai ga wannan matakin, ita ce tambayar da na yi wa shugaban 'yan kasuwa na karamar hukumar mulkin Illela, wanda ya yi bayani kamar yadda za a ji a sauti.

A dai kasuwar Illela da ma garuruwan da ke kan iyaka da Nijar daga bangaren Najeriya matsalar canjin Naira ta kai wa kowa karo. Da zaran ka shiga wadannan garuruwan na Najeriya da ke kan iyaka da jamhuriyar Nijer, yan kasuwa kan nuna kyama ga tsofin kudaden ne na Najeriya, yayin da sabbin kudaden, kama daga yan canji da yan kasuwa, suka koma yin kudin da ruwa da su, domin, zaka bada jikka ta sefa a baka naira 700, yayin da za a iya yi maka taransfa a naira dubu da 170 kowace jikkar sefa.

Wani dan kasuwar wake a Karamar Hukumar Mulki ta Gada ta jahar Sokoto Tarrayar Najeriya, ya yi mini bayyanin yanda lamarin kasuwancin ke tafiya ala tilas sai da kudaden sefa, kamar yadda za a ji ta sauti.

Sabbin kudin Naira

Shi ma wani mai sana’ar babura a Karamar Hukumar Mulkin ta Gada, ya ce lamarin na kudade a garuruwan su dake iyaka da Jamhuriyar Nijar, ya koma aiki ne da kudaden sefa.

Yan kasuwa da dama ne a iyakar Nijar da Najeria, da yan canji suka koma sana’ar kudi da ruwa, ta hanyar fakewa da wannan matsalar ta canjin kudaden naira ta Tarrayar Najeriya

Saurari rahoton Harouna Mamane Bako:

Your browser doesn’t support HTML5

Kasuwar Iyakar Nijar Da Najeriya.mp3