Ja-in-jar da ake yi kan samar da wasu kudaden tallafin rage radadin da annobar coronavirus ta haifar a Amurka, ta sa mafi aksarin kasuwannin hannayen jari a yankin Asiya sun fadi a yau Laraba.
WASHINGTON D.C. —
Kasuwar Nikkei da ke Tokyo ta kare da kashi 0.4, KOSPI ta Seoul ta tashi da kashi 0.5 yayin da TSEC ta Taipei ta fadi da kashi 0.8 yayin da S&P/ASX a Sydney ta yi kasa da kashi 0.1.
Da tsakar ranar yau ne, kasuwar hannayen jari ta Hang Seng da ke Hong Kong ta yi sama da kashi 1.1 yayin da a Shanghai hannayen jarin suka yi kasa da kashi 0.6, sai Sensex ta Mumbai da ta fadi da kashi 0.1
A nahiyar Turai kuwa, hannayen jarin sun yi kasa da sama ne.
FTSE a London ta yi sama da 0.5 sai CAC-40 ta Paris da ta haura da kashi 0.1 yayin da DAX ta Franfurt ta yi kasa da 0.1.