Na farko dai shi ne farashin man fetur da kuma galabaitar da tattalin arziki yayi saboda cutar Coronavirus wadda ke ci gaba da yaduwa a kasashe sama da 100.
Muhimman hada-hadar da aka yi a kasuwar hannun jari a birnin New York jiya dai sun fadi da sama da kashi 7 cikin 100, biyo bayan faduwar kashi biyar cikin 100 a wasu kasuwannin hannun jari na nahiyar Asiya.
Yayin da kasuwannin hannun jarin nahiyar Turai suka tashi da kusan faduwar kashi 8 cikin 100.
Ita kuma Kasuwar hannun jari da aka fi sa wa ido, wato Dow Jones da ke dai-dai da hannayen jarin wasu manyan kamfanonin Amurka 30, ta tashi da maki 2,000 kawai, wanda ke dai-dai da faduwar kashi 7.9 cikin 100.