Kasuwanni Hannun Jari Na Cikin Tsaka Mai Wuya A Duniya

Kamfanin fasahar sadarwa na Apple ya ce cinikin na’urorin shi yayi kasa sosai, sannan darajar kamfanin zata ragu.

A yau dinnan Jumma'a kasuwar hannun jari ta Asiya ta cigaba da tangal-tangal, bayan gargadin da kamfanin wayar hannu na Apple ya yi cewa, ciniki da kuma darajar kamfanin zai ragu, kuma kasuwannin hannayen jarin Amurka za su dan fadi.

Kasuwar kasar Tokyo ta yi kasa da kashi uku cikin dari a cinikin safiyar yau, bayanda kasuwannin Shanghai, Sydney, Seoul, da Taipei suma suka sauka kasa.

Ranar Alhamis Kasuwannin hannun jari su ka sauka kasa a duniya baki daya, bayan kamfanin fasahar sadarwa na Apple ya ce cinikin na’urar shi ya yi kasa sosai a kasar China a watan da ya gabata, wannan shi ya ke nuna alamun akwai faduwa a tattalin arzikin duniya baki daya.

Kamfanin Apple ya danganta musabbabin faduwar jarinsa da takaddamar cinakayyar da ake yi, tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da kasar China, amma Shugaban na Amurka ya kare kansa a shafinsa na Twetter, inda ya rubuta cewa "baitilmalin Amurka ya karbi biliyoyin daloli na haraji daka kasar China da ragowar kasashe a duniya. Dole a dau irin wannan mataki."