Taron na kwana biyu ya hado 'yan kasuwa daga sassan Najeriya daban daban tare da Amurkawa 'yan kasuwa.
Wani Huseini Lamin wanda ya wakilci kamfanin Dantata mai sarafa abinci yana cikin wadanda suka halarci taron da nufin habaka harkokinsu da Amurkawa ta fannin kayan lambu.
Dangantaka tsakanin Amurka da Najeriya ta kara karfafa tun da Muhammad Buhari ya karbi shugabancin kasar.
Ba'amarike dan kasuwa Mark Shiman yace akwai babbar dama ga 'yan kasuwar Najeriya da na Amurka saboda Najeriya babbar kasuwa ce idan aka yi la'akari da yawan jama'arta wajen miliyan dari da saba'in..
Kwanciyar hankalin siyasa da Najeriya ta samu ta sa Amurkawa suna maida hankalinsu Najeriya domin kulla dangantakar kasuwanci da 'yan kasar. Amurkawa zasu soma rububin shigowa kasar saboda kasuwanci.
Wamban Shinkafi Alhaji Sani Abdullahi shugaban kamfanin saka jari na Shinkafi Investment yace idan 'yan kasuwa suka yi anfani da bayanan da aka bayar zasu samu gajiyar taron. Zasu samu garabasa saboda shirin AGOA da LAKAJI (Lagos,Kano,Jibiya). Idan aka yi anfani da bayanan da AGOA ta bayar 'yan kasuwa zasu amfana dashi.
Galibin wadanda suka yi jawabi sun jaddada samun rancen bankin kasuwanci domin kara zuba jari. To amma sai an bullo da wani shiri daban a kawar da bada jingina.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5