KASUWA: Hada Hadar Kasuwanci A Wasu Kasuwannin Jihohin Nijer, Mayu 1, 2022

Yayin da ake hada-hadar sayen kayen masarufi a wata kasuwa a Kano

Shirin kasuwa na wannan makon ya kai ziyara wasu kasuwannin jihohin jamhuriyar Nijer gabanin bukukuwan Sallah.

Washington, DC - ‘Yan kasuwanni daga jihohi dabam dabam, kama daga Maradi, Damagaram, da sauransu, sun bayyana mabambantan ra’ayoyi akan farashin kayayyaki.

Galibi ‘yan kasuwar sun yi korafi akan tsadar kayayyakin masarufi, a wani lokaci da hukumomi suka bada sanarwar sassauta kayayyaki da dama. Bayan tashin farashin kayayyaki wasu ‘yan kasuwar sun ce kalubalen da suke fuskanta shi ne na masu kin biyan bashi.

A yankin jihar Diffa, mai makwabtaka da Najeriya, ‘yan kasuwar sun bayanna damuwa akan yadda kalubalen tsaro ya shafi harkokin kasuwanci a kasuwar N’guigimi, musammna ta bangaren kifi da kayan miya.

Saurari cikakken shirin wanda Souley Mumuni Barma ya gabatar.

Your browser doesn’t support HTML5

KASUWA: Hada Hadar Kasuwanci A Wasu Kasuwannin Jihohin Nijer, Afrilu 30, 2022