KASUWA A KAI MIKI DOLE: Yadda Matsalar Karancin Kudade Ta Shafi Harkar Kasuwanci A Babbar Kasuwar Bodija Da Ke Ibadan, 09 Afrilu, 2023

  • Hasan Tambuwal

Kasuwa a Najeriya

Harkokin kasuwanci da dama sun tagayyara bayan da hukumomin Najeriya suka sauya wa wasu daga cikin kudaden kasar fasali, lamarin da ya haifar da karancin kudaden a hannun jama'a.

Shirin ‘Kasuwa A Kai Miki Dole’ na wannan mako ya leka babbar kasuwar Bodija ta garin Ibadan da ke jihar Oyo inda shirin ya duba yadda matsalar karancin kudade a hannu ta shafi hada-hadar kasuwanci.

‘Yan kasuwar sun yi wa wakilin Muryar Amurka Hassan Umar Tambuwal bayani kan farashin wasu kayayyaki da suke saida wa.

Sai duk da karancin kudin da wasu suka koka akai, wani mai saida kwadi da kirgi ya ce shi kam sai son barka.

Alhaji Ibrahim Nayade Maiyama, ya ce ana sayen nau’in kwado na gwarno sosai saboda yana da dadi kamar kifi. Ya kuma ce a yini yakan yi cinikin kimanin naira dubu casa’in.

Saurari cikakken shirin a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

KASUWA A KAI MIKI DOLE: Yadda Matsalar Karancin Kudade Ta Shafi Harkar Kasuwanci A Babbar Kasuwar Ibadan - 10'00"