Jihar Gombe da ke shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya ta gudanar da wani babban taro na ‘yan kasuwa daga ciki da wajen Najeriya da zummar fadakar dasu kan abubuwan da jihar ta tanada da zasu taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci.
A wata hira da wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad ya yi da gwamnan jihar Gombe Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, gwamnan yayi bayani kan yadda taron zai bunkasa harkokin kasuwancin jihar.
Alhaji Sunusi Abdullahi Lere, shi ne shugaban ‘yan kasuwar jihar Gombe, ya yaba da wannan taro, sai dai ya ce suna bukatar tallafi daga wajen gwamnati don bunkasa harkokin kasuwancinsu.
Samar da kamfanoni da masana’antu da zasu sarrafa albarkatun da ake dasu a kasa na daga cikin hanyoyin bunkasa harkar kasuwanci da kuma samar da ayyuka ga matasan da ke gararamba akan tituna, a saboda haka sarkin shanun Yamaltu, Alhaji Abubakar Bello ya kuduri aniyar samar da kamfanin sarrafa shinkafa da kuma samar da madara daga shanu.
A nasu bangaren, wakilan al’umma sun jaddada muhimmancin duba wasu hanyoyi da zasu taimaka wa gwamnatoci samar da ayyuka ga matasa ta fuskar saye da sayarwa.
Saurari cikakken shirin cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5