Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da asusun na UNICEF ya fitar, inda ya ce Najeriya nada kashi 11 cikin dari na yaran da ba'a yi rijistar haihuwarsu ba a yammacin Africa.
Sanarwar tace yara miliyan 166 ‘yan kasa da shekara biyar da aka haifa a duniya ba’a taba masu rigista ba.
Sanarwar ta kara da cewa nahiyar Africa ke da mafi karancin rijistar haihuwa a duniya, inda kashi 44 cikin dari ake yi musu rijista a lokacin haihuwa, yayin da miliyoyin yara ke mutuwa da ba’a san adadin su ba.
Rijistar haihuwa dai tana kan gaba wajen baiwa ko wani yaro asali na musamman da zai ba shi damar samun ababen mure rayuwa da za su inganta rayuwar sa kamar kiwon lafiya, ilimi da kariya ta zamantakewa.
Wakilin UNICEF a Najeriya Peter Hawkins yace "kowane yaro yana da kima da daraja, kuma dole ne mu tabbatar da cewa muna kidaya kowane yaro domin samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya da Ilimi."
Ya kara da cewa za su yi aiki da sauran hukumomin kamar hukumar kidayar jama'a ta kasa, da ta rijistar 'yan kasa da dukan sauran hukumomi don inganta rigistar haihuwa a Najeriya, saboda yana cikin manufofin ci gaba na majalisar dinkin duniya wato (SDGs).