Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa kashi goma bisa darin al'ummar Ghana na fama da matsalar tabin hankali. Cikin mutane fiye da miliyan uku da ke fama da wannan matsala, akwai wadanda na su ke da sassauci kazalika wasu kuma nasu ya tsananta.
Ministan Lafiya na kasar Ghana, Dr Agyeman Manu ya bayyana hakan yayin da ya gurfana a Majalisar Dattawan kasar a inda ya jaddada rahoton da hukumar ta Lafiya ta Duniya ta fitar tare da cewa dubu goma sha shida cikin masu lalurar tabin hankali a kasar sun bazu a sassan fadin kasar 'wasu na kauyuka da birane.
"Matsalolin tabin hankali sun kasu kashi hudu a Ghana: akwai wadanda suke asibiti, akwai wadanda ke samun kulawar majinyatan gargajiya, kazalika akwai wadanda suke gida ba tare da sanin suna da wannan matsala ba, sai kuma wadanda suka bazu atituna", inji shi.
Wani bincike kuma ya nuna cewa wasu daga cikin masu fama da tabin hankali a kasar Ghana ana cin zarafinsu kamar yi musu fyade ko kashe su domin anfani da sassan jikinsu kazalika wasu kuma ana yi musu dukar tsiya yayin yi musu jinya.
A baya bayannan sai da wani saurayi mai sana'ar gasa biredi ya yi lalata da wata yarinya mai lalurar kwakwalwa mai shekaru 16 da haihuwa mai fama da matsalar tabin hankali a cikin ban daki kamar yadda shaidar gani da ido da ta bukaci da a sakaya sunanta ta gaya ma Muryar Amurka.
"Nayi sallama sai na ji shuru to sai na karasa saboda na dade ina jira... na shiga cikin ban dakin bayan saurayin ya fito , sai na tare da Mabena mai tabin hankali tsirara..ba ta magana.
Na tambayi saurayin, a inda ya tabbatar mini da cewa ya sadu da ita Maabena mai tabin hankali amma ya na roko na da na rufa masa asiri. Ni kuwa na ga ba zan iya ba, sai na fada wa mahaifiyarta" inji matar.
Mallam Abdul Nasir Bychance mai fafutukar kare hakkokin bil Adama musamman wadanda ake tuhuma da maita tare da masu tabin hankali, kana wakilin kungiyar kasa da kasa ta Ghana /Turkey Frienship, yayi kira ga gwamnati da ta yi kokarin samar da asibitoci a sassan fadin kasar sabi da ana muzguna wa masu tabin hankali a kasar musamman wadanda ake zarga da maita.
Shi kuwa Mallam Muhammad Bashir da' dansa ke fama da matsalar tabin hankali ya ce suna shan wahala sosai kafin su kai asibitin Ankaful a jahar tsakiya daga Kumasi a Ghana saboda nisar asibitin kuma yanayin asibitin ba ya da kyau.
Ministan lafiya na kasar, Dr Kwaku Agyemang Manu ya jaddada matakan da gwamnatin kasar ke daukawa domin shawo kan wannan matsala a inda yake cewa:
"Abin da muke yi ayanzu shi ne mu fadada kula da masu fama da lalurar tabin hankali a fadin kasar ya kasance an samu likitoci na masu fama da matsalar tabin hankali a kowani asibiti. Hakan zai taimaka sosai. Gwamnati zata gina karin asibitocin masu fama da tabin hankali guda 3 nan bada jimawa ba", inji shi.
Ghana na da asibitocin masu fama da tabin hankali guda 3 da suka hada da: Pantang Psychiatric Hospital, Accra Psychiatric Hospital, and Ankaful Psychiatric Hospital.
Saurari cikakken rahoton Hamza Adam daga Kumasi, Ghana:
Your browser doesn’t support HTML5