Kasashen Yankin Asiya Sun Fi Amfani Da Yanar Gizo A Duniya

Wani sabon bincike da kamfanin Google ya kaddamar, ya bayyanar da cewar kasashen yankin kudu maso gabashin Asiya, su suka fi amfani da yanar gizo a fadin duniya, musamman wajen amfani da wayar hannu. Rahoton ya kara da cewar adaddin kudin da ake kashewa wajen sayan intanet ya haura dalar Amurka biliyan $100 a wannan shekarar.

Mutane a babban birnin Thais, na amfani da yanar gizo akalla na sa’o’i 5 kowace rana, fiye da sa’o’i 4 da mutane keyi a kasashen Indonesia, Philippines, da Malaysia, sauran kasashe kuwa a fadin duniya ana amfani da yanar gizo ne akalla na sa’o’i 3 a kowace rana.

Wannan na nufin cewar mutane na kwashe tsawon lokacin akan shafukan yanar gizo, fiye da yadda sauran mutane a fadin duniya. Kamfanin na Google tare da hadin gwiwar wani kamfani Temasek, sun kwashe shekaru suna gudanar da wannan binciken na makudan kudade da ake kashewa akan yanar gizo a yankin kasashen Asiya.

Mutane a yankin na amfani da yanar gizon ne wajen, amfani da na’ura mai dauke da taswirar duniya ta GPS, karance-karance labarai, da kallo ko saka tallace-tallace a shafukan zumunta, shiga motocin haya, siyayya a shafukan kamfanoni, kai harma da aikawa ko karbar kudade daga bankuna wajen amfani da yanar gizo.