Shugabannin kasashen turai sun yi taron gaggawa a Brussels saboda matsalar 'yan gudun hijira daga Syria da take neman zaman masu kayar kifi.
WASHINGTON DC —
A jiya Labara, shugabannin kungiyar tarayyar Turai suka yi taron gaggawa a Brussels game da babbar matsalar kwararar ‘yan gudun hijira.
Shugabannin na neman hanyar da za su sa ido a kan iyakokin kasashensu. A daidai lokacin da kuma suka baiwa Turkiyya da wasu kasashen da suka karbi ‘yan gudun hijirar sabon taimakon agaji.
Har yanzu akwai rarrabuwa kawuna tsakanin Shugabanin kasashen Turan game da yadda za su yi da dubban masu neman mafaka a Turai don gujewa bala’in yakin Syria a Gabas ta Tsakiya.
Duk kuwa da yadda Ministocin harkokin cikin gidan kasashen Turan suka kasafta rabon ‘yan gudun hijira guda dubu 100 da 20 a tsakanin kasashensu guda 28.