Kasashen Turai Sun Tura Wa Iran Kayayyakin Jinyar Marasa Lafiya

Kasashen Jamus, Birtaniya da Faransa sun fitar da kayayyakin asibiti da na jinyar marasa lafiya zuwa kasar Iran karon farko, ta hanyar wani tsari na kauce wa takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran, a cewar Jamus a yau Talata.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Jamus ta fitar a yau Talata, bata bayyana irin nau'in kayayyakin asibitin ba, ko kuma kamfanonin da suka taimaka wajen tura kayayyakin.

Sanarwar ta kuma ce yanzu tunda wannan tsarin yayi nasara, bangarorin biyu za su yi aiki akan karin wasu abubuwan.

A shekarar 2015 ne Iran da wasu manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya su biyar suka rattaba hannu kan yarjejeniyar takaita shirin nukiliyar Iran don ita kuma Iran din ta samu sassaucin takunkumi.

Bayan da Amurka ta janye daga yarjejeniyar kuma ta kakaba takunkumi kan Iran, Iran ta matsa wa sauran kasashen Turai da suka sanya hannu a yarjejeniya lamba akan su nemi hanyar kaucewa takunkumin don tallafawa tattalin arzikin kasar da ya fuskanci koma baya.