Sakataren ma'aikatan tsaron Najeriya Isma'il Aliyu shi ya yi jawabi jiya a madadain hafsan hafsoshin Najeriya Air Marshal Alex Badeh a taron hafsan hafsoshin kasashen gabar tafkin Chadi da ya kawo karshe.
Sakamakon taron shi ne samun kwamanda daya da duk sojojin hadin gwiwa da zasu yaki Boko Haram da ta'adanci a yankinsu. A taron, Najeriya tayi alkawarin bada gudummawar dala miliyan dari domin gudanar da aikin. Da can baya kasashen waje ne suke bada taimako duk da cewa yawancin fadan Boko Haram cikin Najeriya ake yinshi.
Taron ya nuna mahimmaancin da shugabannin kasashen suka baiwa taronsu da nufin samun zaman lafiya a yankin. Yanzu sojoji sun hada kai. Haka ma shugabannin kasashen da sakatarorinsu su hada kai su yaki ta'adanci.
Babban sakataren hukumar tafkin Chadi dake da hedkwata a Njemina Injiniya Sanusi Imrana yayi karin bayani akan kudaden da ake bukata saboda ayukan tsaro a wasu wuraren da suka fi dandana rikicin Boko Haram.Yace ana bukatar sefa biliyan talatin da takwas da rabi. Zasu ba shugabannin kasashen shawara cewa a yi aikin gaggawa cikin watanni 18 a wuraren da suka fi lalacewa saboda Boko Haram. Za'a kirkiro ayyuka kanana da zasu taimaki matasa su samu aikin yi. Wasu ana iya basu jari. Wasu kuma kayan aiki za'a basu.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5