Myanmar da Bangladesh, sun rattaba hanu akan wata yarjejeniyar maido da daruruwan dubban ‘yan kabilar Rohingya, wadanda suka tsere zuwa Bangladesh domin gujewa azabtar da su da ake yi a jihar Rakhine da ke Myanmar, a cewar hukumomin kasashen biyu.
Myint Kyain, wanda Sakatare ne na Dindindin a ma’aikatar da ke kula da harkokin kwadago da kaurar jama’a da kuma yawan al’uma a kasar ta Myanmar, ya ce an rattaba hanu akan wata yarjejeniyar fahimtar juna a jiya Alhamis, ba tare da bada wani karin haske akan yarjejeniyar ba.
Sama da Musulmi ‘yan kabilar Rohingya dubu 600 ne suka tsallaka zuwa sansanonin ‘yan gudun hijra da ke Bangladesh.
Kasar ta Bangladesh, ta ce, nan da watannin biyu masu zuwa za a fara aikin kwaso ‘yan Rohingyan.