Kasashen Duniya Na Ci Gaba Da Rige-rigen Zuwa Duniyar Wata

Kwanaki kadan da shiga sabuwar shekarar 2020, India ta bayyana aniyyarta ta sake wani yunkurin zuwa duniyar wata a wannan shekara.

Kokarin da ta yi a bara na aikawa da wani jirgin sama jannati da ba ya dauke da kowa a bara ya cutura.

Shugaban hukumar kula da fannin binciken sararin samaniyar kasar ta India ne ya bayyana wannan sabon yunkuri.

“Aiki na tafiya “daidai” akan jirgin “Chandrayaan-3 domin tura shi duniyar wata” a cewar shugaban hukumar, Sivan K.

Ya kara da cewa, “muna sa ran a wannan shekarar za mu tura wannan jirgi, amma babu mamaki aikin ya shiga shekara mai zuwa.”

Wasu majiyopyi kwarara sun ce a watan Nuwamba ake sa ran kammala aikin.

Jirgin sama jannatin da Indian ta kera mai suna “Chandrayaan-2, ya fado kasa a watan Satumba, abin da ya kasance koma baya ga kasar.