Kasashen Afirka 14 renon kasar Faransa ne ke anfani da kudin takardar sefa.
Kasashe takwas na yammacin Afirka ne yayinda shida na tsakiya. A hukumance kudaden sun fara aiki ne a ranar 26 na watan Disambar shekarar 1942 koda yake wasu kasashe uku sun taba ficewa kafin daga bisani su koma.
Shin me ya sa kasashen renon Faransa ke cigaba da yin anfani da kudin sefa sabanin kasahe renon Ingila dake anfani da nasu kudin?
Dr Soni Abdullahi ya bayyana dalilin hakan. Yace lokacin samun 'yancin kai kasashe renon Ingila suna da kudin Ingila amma su da aka zo batun samun 'yancin kai sai suka yi yarjejeniya da Faransa cewa koda ma sun samu 'yancin kai zasu cigaba da yin anfani da kudin da Faransa ta kirkiro masu.
Amma kasashe renon Ingila suka ce babu wani 'yanci idan kasa ba zata iya kirkiro nata kudin ba.
A cewar Dr Abdullahi da wuya kasar Faransa ta bar kasashen da ta rena su samu kudin kashin kansu idan aka yi la'akari da ribar da Faransa ke samu sanadiyar kudin sefa. Yace kafin Faransa ta bada kudi sai kowace kasa ta ajiye kashi arba'in a babban bankin kasar Faransa din.
Yanzu dai shugabannin kasashen sun yanke shawarar kirkiro da nasu kudin nan da zuwa shekarar 2020.
Ga rahoton Yusuf Abdullahi da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5
Sirajo Isiyaka masanin had hadar kudade yace lokaci yayi da kasashen zasu hada kansu su samar ma kansu nasu takardun kudin domin tabbatar da 'yancinsu. A yanzu sai abun da Faransa ta ga dama ta keyi da kudin sefa din