Yanzu haka kasashe 6 ne suka fara wani taro a Pakistan domin duba yadda zasu tuinkari kalubalen ayyukan taaddanci da kuma hadin kai tsakanin su.
Kakakin majilisar dokokin kasashen Pakistan, China,Russia,Turkiyya,Afghanistan, da Iran, sune ke jagorantar tawagar kasasahen su wajen wannan taron.
Kuma ana gudanar da taron ne karkashin tsastsauran matakan tsaro a babban birnin kasar na Pakistan.
Shugaban majilisar dattawan kasar Pakistan Raza Rabbani yayi anfani da wannan taron wajen mayar wa gwamnatin Amurka Martani
Rabbani yace sun gani a cikin ‘yan kwanaki biyu da suka gabata mataimakin shugaban kasar Amurka har yana da kwarin gwiwar da ikon cewa ya saka kasar Pakistan a ciki kasashen da ake sawa ido,
Shugaban majilisar yace to bari ya fadi da babban murya kuma duniya ta saurara Pakistan kasa ce me cikakken ‘yancin cin gashin kai.
Haka kuma yace kasar bata karban umurni daga hannun kowa, balle ma Amurka.
Wadannan kalamai na Rabbani dai suna nufin amsa ce kai tsaye ga kalaman Mike Pence.
A lokacin da yake wa sojojin Amurka jawabi sailin da yakai ziyara a Afghanistan ranar alhamis.
An jiwo Pence nacewa Pakistan ta jima tana baiwa ‘yan taadda irin su Taliban da sauran kungiyoyin ‘yan taadda mafaka.
Awannan taron gwamnatin kasar Pakistan tayi anfani dashi domin mayar wa Pence da martini.