Kasashe 5 Sunyi Marhabin da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Afghanistan

Kasashe 5 da ke kokarin ganin an sasanta rikicin Afghanistan, sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa, da ke marhabin da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka yi domin gudanar da shagulgulan Sallah a kasar, tare da kiran bangarorin biyu da su dora akan matakin.

“Muna kara karfafawa bangarorin 2 gwiwa da su ci gaba daga wannan shirin na sulhu zuwa makwannin gaba ba tare da bata lokaci ba. Masu shiga tsakani na burin ganin an kawo karshen takaddamar a kasar ta Afghanistan”, a cewar sanarwar ta hadin gwiwar kasashen Qatar, Jamus, Indonesia, Norway da Uzbekistan a jiya Lahadi, ranar da ake bikin Sallar Idil Fitr a Afghanistan, daya daga cikin bukukuwan ibada masu daraja a addinin Islama.

Sanarwar ta biyo bayan wata sanarwa da kugiyar Taliban ta fitar na tsagaita wuta ta tsawon kwana uku daga jiya Lahadi.

Shugaban kasar Ashraf Ghani, ya maida martani ta hanyar tsagaita wuta a nashi bangare, tare da sakin fursunoni 2,000 ‘yan kugiyar Taliban.

Kungiyar Taliban na bukatar a saki fursunoninta har 5,000, kamar yadda aka yi matsaya a jarjejeniyar da aka cimma da Amurka kamin su amince da zaman sulhu.

Ana sa ran sulhun zai kai ga samar da dawwamammen zaman lafiya mai daurewa, da samar da tsarin gwamnati ta dukkan ‘yan kasar Afghanistan da suka hada da ‘yan kungiyar Taliban.