Gwamnatin Uganda ta rattaba hannu kan wata yarjajjeniya da kamfanin man Tullow na Burtaniya ta hako albarkatun man fetur da iskar gas a kasar.
Ministan Makamashi Hilary Onek ta ce wannan yarjajjeniyar ta warware batun harajin da aka dade ana takaddama akai wanda hakan ya kawo tsaiko ga tsare-tsaren kamfanin na Tullow.
Kamfanin na Tullow ya sayi akasarin hannun jarin abokin hada hunnunsa a kasuwancin wato Heritage Oil a farkon shekarar da ta gabata. To amman gwamnatin Uganda ta bukaci kamfanin na Heritage ya biya dala miliyan 404 a matsayin harajin da aka samu daga cinikin, wanda kamfanin kuma ya ki amincewa.
Onek ya ce yarjajjeniyar ta ranar Talata ta gamsar da gwamnati, ta kara da cewa kamfanin na Tullow zai biya dala miliyan 469 a matsayin haraji zuwa karshen wannan watan.
Za a kuma amince wa kamfanin ya kawo wasu abokan huldar kasuwanci biyu cikin wannan harkar, wato kamfanin man Faransa mai suna Total da Kamfanin Man China mai suna China National Oil Corporation, CNOOC.
Gwamnatin Uganda ta yi kiyasin cewa akwai albarkatun mai a karkashin kasa a yankin Albertine na yammacin kasar kimanin ganga biliyan 2.5.