Kasar Turkiya Ta Gurfanar da Wasu Janar-janar 26 Gaban Kotu

Kwamandan Mayakan Sama Janar Akin Ozturk, na cikin wadanda aka gurfanar gaban kotu da ake zarginsu da yunkurin kifar da gwamnantin kasar bara

A kasar Turkiya, an soma shara’ar mutane 220 da suka hada da manyan hafsoshin soja 26 masu mukaman janar-janar, wadanda ake zargi da taka rawa a yunkurin juyin mulkin da aka so yi a watan Yulin shekarar da ta gabata.

Daga cikin wadanda aka gurfanar a gaban kotu harda General Akin Ozturk, tsohon babban kwamandan mayakan jiragen sama na kasar.

Turkiya dai tana zargin wani hamshakin malami dan kasar Turkiya dake zaune a nan Amurka mai suna Fethullah Gulen da laifin kitrsa makircin yunkurin juyin mulkin na ran 15 ga watan Yulin 2016, wanda mutane fiyeda 260 suka rasa rayukkansu a cikinsa.

Gulen dai ya musanta zargin cewa yana da hannu cikin lamarin.

A jiya Lahadi ne kuma shugaban Turkiyar, Recep Tayyip Erdogan ya kara tsawaita dokar ta-bacin da aka kafa tun bayan yunkurin juyin mulkin na bara.

A karkashin wannan dokar-ta-bacin ne aka kame mutane fiyeda 47,000, sannan an kori wasu 100,000 daga aiyukkansu a bisa tuhumar cewa sun taka rawa cikin yunkurin.