Hukumomin Kasar Spain sun fara zargin mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho tare da wakilinsa Jorge Mendes na rashin biyan wasu haraji a kasan a lokacin yana mai horas da kungiyar Real Madrid.
Indai ba'a mantaba a satin da suka wucene kasar ta Spain ta zargi shahararren kuma gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Cristiano Ronaldo akan rashin biyan wasu haraji da kudin ya kai kimanin fam miliyan 14.
Wanda sanadiyar wannan zargi yasa dan wasan ya ceri sha'awarsa na zama a kungiyar ta Real Madrid.
Haka kuma a shekarar da tawuce ne hukumar kasar ta Spain ta gurfanar da dan wasan Barcelona Lionel Messi a gaban kutu inda take tuhumarsa bisa kin biyan haraji wanda daga karshe har kotu ta yanke masa biyan tara da kuma zaman gidan yari na shekaru biyu.
Masana kwallon kafa a duniya na ganin yin hakan zai iya kawo tabarbarewar kwallon kafa a kasar ta Spain, inda suke ganin nan gaba kadan yan wasan kwallon kafa bazasuyi sha'awar zuwa wata kulob a kasar ba don taka leda ganin yanda akeyi wa ‘yan wasa bayan an ci moriyarsu.