Kasar Sin ta sake zabge darajar kudinta kasa da na Amurka

Yuan, takardar kudin kasar Sin

Kasar Sin ta sake barin darajar takardar kudinta ta na Yuan ta sake faduwa kasa da dala a kwana ta uku a jere.

Yau Alhamis ne babban Bankin kasar ya rage darajar kudin da kashi 1% daga ta jiya, inda ta zama Yuan 6 da kwabbai 40 akan dala 1. Gwamnatin China na sa ido sosai kan darajar Yuan, wadda ta kan barta ta yi sama ko kasa da kashi 2% daga matsayin da ta ke so, wanda ta kan canza shi kullum.

Zuwa yanzu dai takardar kudin ta rasa wajen kashi 4% tun karon farko da aka fara canza matsayinta a kasuwar hada-hada. Bankin ya fadi a wannan satin cewa an yi abin da ya kira, "gyara sau daya" don a bar kasuwa ta rinka yin tasiri sosai wajen auna darajar Yuan.

To amma masu saka jari da dama na fargabar cewa, katsalandan din da ake a fagen tattalin arzikin wannan kasa, wacce ita ce ta biyu a girman tattalin arziki a duniya, ya kawo tafiyar hawainiya fiye da yadda aka hanga a baya.

Akwai kuma fargaban cewa hakan na iya sa wasu kasashen su ma su rage darajar takardun kudinsu, tunda rage darajar Yuan zai sa a yi ribibin kayan da aka sarrafa a kasar ta Sinawa.