Pakistan Zata Sake Duba Tsatstsamar Alakarsu Da Amurka

Tun a watan fabrairun shekarar 2018 din nan da muke ciki ne, cibiyar kula da harkokin kudade da ke Paris wacce ake kira FATF a takaice, ta yanke shawarar sanya Pakistan a cikin rukunin kasashen da basa mai da hankali wajen yaki da ta’addanci.

Kasar Pakistan tace zata sake duba dangantakarta da Amurka da tuni dama tayi tsami, matakin da zai iya dakatar da shigar da kayayyaki zuwa Afghanistan inda dakarun Amurka da taimakon kasashe kawayen rundunar NATO ke yakar ‘yan ta’adda domin kawo zaman lafiya a kasar da yaki ya daidaita.

Ministan harkokin wajen Pakistan Khurram Dastgir Khan ne yayi wannan bayanin kwana daya kafin dakarun kasa da kasa su sanya kasar a jerin sunayan da ake sa wa idanu akan samar da kudaden ta’addanci bisa umurnin gwamnatin, matakin da ka iya kara tabarbarar da tattalin arzikin Pakistan.

Hukuncin da Amurka ta yanke na cikin dabarun Trump na yankin Asiya da ya sanara watan Agusta don hurawa Pakistan wuta ta su yanke alaka duk wata alaka da ake zargi tana da iata da ‘yan Taliban da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke ta kaddamarda munanan hare hare kan sojojin Amurka dake Afghanistan.