Kasar Morocco Bata Cikin Jerin Kasashen Da Zata Karbi AFCON

Rachid Talbi Alami, Ministan wasannin kasar Morocco, ya bayyana cewar kasarsa ba ta cikin jerin kasashen dake neman karban bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta Nahiyar Afrika AFCON na shekara 2019.

Ministan ya fadi hakan ne yayin hirarsa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

Kafin kalaman ministan wasannin na kasar ta Morocco, rahotanni sun sha bayyana cewar kasar Morocco da Afrika ta Kudu na rukunin kasashen da suke kan gaba wajen zawarci samun damar karbar bakoncin gasar cin kofin Nahiyar ta Afrika, wanda za'a fara a ranar 15 ga watan Yuni 2019.

Gasar ta AFCON ta canza salo inda a yanzu kasashe 24 za su fafata, maimakon kasashe 16 da suka saba halartar gasar a shekarun baya.

A watan da ya gabata ne dai hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Nahiyar Afrika CAF, ta amshe damar karbar bakoncin gasar daga hannun kasar Kamaru, bisa dalilai na rashin kammala shirye shirye da kuma matsalolin tsaro.