Kasar Masar Za Ta Karbi Bakoncin Gasar Zakarun Kasashen Afrika

A yanzu ya tabbata cewar Kasar Masar ce za ta karbi bakoncin Gasar cin
Kofin Kasashen nahiyar Afirka a bana 2019, kamar yadda hukumar da ke kula da wasannin kwallon kafa ta Afrika CAF ta bayyana ranar talata 8/1/2019.

Kasar ta Masar ta doke kasar Afrika ta Kudu ne, wacce ita ce kasa da tayi takara da Masar wajan karban bakoncin gudanar da gasar, a wani taron da kwamitin zartarwa yayi a kasar Senegal.

A baya dai kasar Kamaru ce za ta karbi bakoncin gasar a bana, sai dai kuma a watan Nuwamba 2018 hukumar ta CAF, ta kwace damar saboda abin da ta bayyana da cewar, Kamaru tana tafiyar hawainiya wurin gudanar da shirye shiryenta na karban gasar, da kuma al'amuran da suka shafi tsaro a kasar.

Wannan shine karo na biyar da kasar Masar za ta karbi bakoncin gasar, inda yanzu ya rage mata watanni shida kawai kafin a fara gasar, za'a fara gasar ne a watan Yunin bana. A bana dai hukumar ta CAF ta shirya cewar kasashe 24 ne za su fafata a gasar.