Kasar Malasiya Za Ta Tura Sojoji Somaliya

  • Ibrahim Garba

Shugaban Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed (Farmajo)

A wani al'amari na bazata, kasar Malasiya na shirin tura wasu sojojinta zuwa kasar Somaliya don su taimaka da, abin da ta kira ayyukan agaji.

Kasar Malaysai za ta tura sojoji Somalia, a matsayin wani bangare na aikin jinkai, na yinkurin kawar da tsananin rashin abinci don ceto dubban mutane, a cewar jami'an gwamnatin Somaliya da na diflomasiyya a jiya Asabar.

"Ina mai tabbatar da wannan rahoton kuma za a yi cikakken bayani lokacin da tawagar Mataimakin Firaministan Somaliya, Mohammed Omar Arte, wanda ke ziyara a Malaysia, ta koma gida," a cewar Ministan Sadarwa Mohammad Abdi Hayir Mareye, ga Sashin Somaliyanci na Muryar Amurka.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a birnin Kuala Lumpur, Ministan Tsaron Malaysia Datuk Seri Hishammuddin ya ce kasarsa za ta tura manyan jami'an soja uku da kuma dakaru 17 daga bangaren kiwon lafiya na sojojin saman kasar zuwa Somaliyar.

"Su kuma sojojin kasa, wadanda su ka kunshi wani babban jami'i da dakaru 10, za su rika bayar da kariya ga tawagar. Za a yi jigilar kayan abinci da magunguna zuwa Somaliyar ne da jiragen sama samfurin Hercules C-130," a cewar Ministan.