Kasar Malaisiya Ta Kori Jakadan Koriya Ta Arewa

  • Ibrahim Garba

Jakadan Koriya Ta Arewa a Malaysia Kang Chol

Rikicin Koriya Ta Arewa da kasar Malaysia, wanda ya samo asali daga takaddamar da ta biyo bayan kisan wani dan uwan Shugaban Koriya Ta Arewa a Malaysia ya kara tsanani.

Kasar Malaysia ta kori Jakadan kasar Koriya Ta Arewa, a cigaba da rigimar da ake yi sanadiyyar kashe wani dan uwan Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jung Un a filin jirgin saman Kuala Lumpur a watan jiya.

A wata takardar bayani, Ma'aikatar Harkokin Wajen Malaysia ta bayyana jakadan da "abin gujema wa," bayan da ya yi suka kan binciken da ake yi game da kisan.

Malaysia ta aika da sako ga Ofishin Jakadancin Koriya Ta Arewa jiya Asabar, inda ta bayyana ma Jakada Kang Chol cewa ya fice daga kasar cikin sa'o'i 48.

Bayanin ya kuma ce kasar ta Malaysia ta bukaci rokon gafara daga Koriya Ta Arewa, saboda cukarta da ta yi, amma ta ki yi.

An shafa ma Kim Jong-Nam wata mummunar guba mai lahani ga hanyoyin sokonnin jiki. Koriya Ta Kudu na zargin Koriya Ta Arewa da kisan, yayin da ita kuma Koriya Ta Arewa ke bayyana binciken da wani abin da abokan gabarta su ka shirya, da zummar cimma wata manufa ta siyasa.