A wata hira da aka buga a mujallar Bild ta kasar Jamus, Gjorge Ivanov, ya ce batun kwararar bakin hauren ya gunduri Macedonia, bayan da suka ayyana matsalar a matsayin wani babban al’amari da ya sha kan kasar.
Ya kara da cewa kungiyar ta tarayyar Turai, ba ta ba kasar ko sisin kwabo ba, yana mai zargin cewa kungiyar ta rasa alkibla game da batun matslar tsaro da kwararar bakin hauren da suka fito daga Syria da Afgahnistan da Iraqi ka iya haifarwa, da kuma batun matsalar tattalin arziki.
Ya zuwa yanzu kasar ta Macedonia ta karbe paspo dubu tara na bogi ko kuma wadanda aka sato in ji shugaban na Macedonia, ya kuma zargi kasar Jamus da kin gabatar mata da bayanan kwakwaf na mayakan IS.
Sai dai ya ce dangane da batun nuna jin kai kasar ta Jamus ta yi kokari, amma a fannin tsaro ta yi kasa a gwiwa.