Cibiyar nazarin magunguna ta Kenya, dake zaman cibiyar nazarin magani mafi girma a Afrika ta Gabas tana gwajin ingancin wani magani gargajiya da ake kira Zedupex.
Binciken maganin cutar coronavirus da na rigakafinsa ya kara kaimi a fadin duniya, ciki har da Kenya, inda masu bincike suka himmantu wurin samun magani na cikin gida.
Dr. Fetus Tolo na cikin nazarin magani ta kasar Kenya, shine babban jami’in kimiya dake jagorantar masu binciken a kan gano ko maganin itatuwa zai magance COVID-19. Maganin Zedupex da masu nazarin na Kenya suka yi shi a 2015, an yi amfani da shi wurin jinyar cutar kurajen baki ko na kan al’aura.
Tolo ya ce ya zuwa yanzu shi da abokan aikinsa basu iya gano ko cutar za ta magance coronavirus ba.
Duk da kalubalen da ake fuskanta a wannan nazarin, masu binciken a cibiyar ta Kenya sun dukufa wurin samun maganin cikin gida na COVID-19.
Kenya dai tana mutum sama da dubu daya da aka tabbatar da suna da coronavirus kana tuni wasu hamsin suka mutu da cutar.