Kasar Kamaru ita ce ta farko cikin kasashen Afirka ta tsakiya wurin noman ayaba wadda take fitarwa zuwa kasashen duniya.
Saboda ingancin ayabar kasar Kamaru ya sa 'yan kasuwan kayan gwari suke shigar da ayabar cikin wasu kasashe.
Sarkin ayaba na kasashen nahiyar Afirka ta tsakiya Alhaji Muhammad Mustapha PRP. Yace a matsayinsu na 'yan kasuwa suna sayen ayaban suna kuma sayarwa. Daga Kamaru suna aika ayaba zuwa Najeriya bisa ga yarjejeniyar da suka yi da hukumomin kwastan.
Shi ma sarkin ayaba na tarayyar Najeriya Alhaji Hassan ya yi karin haske. Ya tabbatar suna sayen ayaba daga Kamaru ta hannun Alhaji Mustapha PRP wanda yake turo ta Najeriya ta hannun wani Alhaji Muhammad a Calabar. Shi kuma daga Calabar ya zaba zuwa Abuja, Maiduguri,Kano da dai sauran wasu wurare. Ayabar Kamaru nada kyau kuma tana da inganci.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5