Mataimakin Jakadan kasar Japan a Najeriya Mr. Mesaya Otunka ne ya bude azuzuwan karatun a madadin gwamnatin kasar Japan.
Mataimakin jakadan yace ilimi shi yafi komi ga kananan yara. Ilimi kuma yana da mahimmanci wajen bunkasa tattalin arzikin kasashenmu. Jakadan ya kara da cewa gwamnatin Japan tana taimakawa kasashe domin su zaburar da tattalin arzikinsu.
Gwamnan jihar ta Oyo Sanata Abiola Ajimobi yayinda yake jawabi wajen bude azuzuwan ya jaddada dimbin anfanin ilimi ga kasa da jama'arta domin cigaba.Yace ilimi a wurinsu shi ne komi, shi ne kuma kashin bayan cigaban kasa.
Tun shekarar dubu biyu da biyar ne ita gwamnatin Japan take gina azuzuwan karatu da bada horo a sassan Najeriya don habaka ilimi a kasar. Jihohin da suka anfana da shirin na Japan sun hada da Neja, Kaduna, Filato da Kano.
Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5