Jamus zata kafa rundunar sojojin nata ne a birnin Yamai da zummar kara karfafa sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD dake kasar Mali.
Wannan matakin na Jamus ya kara jaddada irin dangantakar dake akwai tsakaninta da kasar Nijar inji jakadan na Jamus.
To saidai tuni masu sharhi akan alamuran yau da kullum suka fara bayyana ra'ayoyinsu akan wannan anniyar ta kasar Jamus. Alhaji Salisu Ahmadu wani kusa a kungiyar dake kishin kasa mai adawa da kafa sansanin sojin wata kasa a Nijar yace yakamata kasar tayi takatsantsan. Yace turawan sun san abun da suke so, Nijar ce bata san abun da take so ba. Jamus zata yi anfani da kasar Nijar ce kawai ta ci riba.
Domin jin karin bayani daga bangaren gwamnatin Nijar kakakin gwamnatin Asmaila Malam Isa ya ki yace komi domin a cewarsa batu ne da ya shafi tsaro. Shi ma ministan tsaro da aka tuntubeshi yace yana cikin wani taro.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5