Prime Ministan Iraqi Hader Al-Abadi ya bayyana yau asabar cewa yakin da aka kwashe shekaru 3 anayi na kokarin ganin an fatattaki ‘yan kungiyar is, ana iyacewa ya cimma nasara, kuma yazo karshe.
Yace yanzu haka sojojin su na Iraqi sune keda cikaken ikon bakin iyakar Iraqi da Syria, don haka yace yana farin cikin bayyana kawo karshen wannan yaki da Daesh.
Abadi yana Magana a wajen wani taron da kungiyar ‘yan jarida suka shirya a Bagadaza.
Wannan labarin na shugaba Abadi yana zuwa ne kwanaki biyu bayan da kasar Rasha ta bayyana cewa ta shawo kan kungiyar ta IS, dake cikin Syria, wadda damar sojojin ta ke marawa sojojin Syria baya.
Gwamnatin kasar ta Iraqi tace wannan nasarar yana nufin cewa yanzu sojojin ta ne keda ikon kudancin kasar hadi da bakin iyakar Iraqi da Syria.
A wani lokaci can baya kungiyar IS ce ke rike da kusan kashi ukku cikin na Iraqi tun a cikin shekarar 2014, inda kungiyar ta zame babban barazana ga kasar ta Iraqi a wannan lokacin, Amma cikin shekaru ukku da rabi da suka gabata kasar ta Iraqi da goyon bayan sojojin da Amurka ke jagoranta suka shiga kassara kungiyar ta IS.