Alamu sun nuna cewa kasar Iran ba zata mika wuya ba game da yarjejeniyar da aka cimmawa da ita a cikin shekarar 2015 game da shirin ta na makamin nuiliya ba, duk ko da matsa mata da Amurka keyi
WASHINGTON DC —
Kasar Iran ba za ta mika wuya ba, duk kuwa da hantararta da Amurka ke yi, game da yarjajjeniyar nukiliyar da aka cimma a 2015, wadda Shugaba Donald Trump ya yi barazanar sokewa, a cewar Shugaban addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei, a jiya Lahadi.
"Kasar Iran na tsaye daram, kuma muddun kasar nan mai danniya ta dau wani matakin da bai dace ba game da yarjejjeniyar nan ta nukiliya za ta fuskanci martanin Janhuriyar Musulunci," a cewar Khamenei a wani jawabinsa ga jami'an 'yan sanda.