“Zuwa yau dinnan, zan iya tabbatar da cewa Iran na kiyaye alkawarin da ta yi game da batun nukiliya a karkashin yarjajjeniyar nukiliya,” a cewar Yukiya Amano, Shugaban hukumar ta hana yaduwar makaman nukiliya, a wani taron manema labarai da aka yada a gidan talabijin na gwamnatin kasar.
Wannan sanarwar ta zo a daidai lokacin da ake takaddama tsakanin Amurka da Iran, sanadiyyar kin tabbatarwa da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi a wannan watan cewa Iran na mutunta yarjajjeniyar nukiliyar da ta cimma da manyan kasashen duniya.
Yanzu dai Majalisar Dokokin Amurka na da wa’adin kwanaki 60 na yanke shawarar ko za ta maido da takunkumin da aka kakaba ma Iran a baya wadanda aka dage mata a madadin daina shirinta na nukiliya ko a’a.