Kasar Indiya Na Daukar Matakan Binciken Shari'ar Fyade cikin sauri

Masu zanga zanga kan fyade

Kotun kuma ta ce ya kamata a samar da manyan kotuna da su ka yi tanade-tanade don yara.

Kotun kolin kasar India ta ba manyan kotunan kasar umurnin gudanar da bincike cikin sauri akan fyaden yara, a daidai lokacin da jama’a ke nuna fushinsu akan fyade da kashe-kashen yara mata da kuma wasu hare-haren akan yara kanana da aka yi kwanan nan.

Babban alkalin kotun kolin kasar, Dipak Misra, ya bada umurnin a kafa kwamiti na binciken gaggwa don binciken kararraki cikin sauri, kuma a wasu kotuna na musamman za a yanke hukuncin.

Yayinda rikicin siyasa a India ya yi kamari akan yawan fyade da kisan yara kanana, a watan da ya gabata, gwamnatin kasar ta amince da hukuncin kisa akan duk wadanda aka samu da laifin yiwa yara ‘yan kasa da shekaru 12 fyade.