Kasar Burundi Ta Kori Hukumar Kare Hakkin Bil Adama

Kasar Burindi ta bawa hukumar kare hakkin bil adama watanni biyu da tabar kasar.

Hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kasar Burundi ta ba ta umurnin ta rufe ofishinta jakadancinta da ke kasar.

A yau Alhamis, mai magana da yawun hukumar Ravina Shamdasani ta ce, sun samu wasikar ne a jiya Laraba, inda aka nemi da su rufe ofishinsu.

Wannan umarnin da aka ba hukumar, na zuwa ne watannin bayan da shugaban hukumar ta kare hakkin bil adama ta ce, “Burundi na daya daga cikin kasashen da ake yawan kashe jama'a ‘yan kwanakin nan.”

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Burundi da wata majiya daga majalisar Dinkin Duniya sun ce, an ba hukumar watanni biyu ta tattara inata-inata.