Kasar Burundi ta yi shelar dakatar da gidajen rediyon Muryar Amurka da BBC daga yada labarai a kasar na tsawon watanni shida, makwanni biyu gabanin kada kuri’ar jin ra’ayin jama’a da za a yi a kasar kan batun kwaskware Kudin tsarin mulkin kasa, ciki har da batun canza tsawon wa’adin Shugaban kasa.
Hukumar Kula da yada labaran kasar ta Burundi, wadda ta zargi Muryar Amurka da BBC da saba ka’idar yada labarai, da kuma gudanar da wasu abubuwan da ta kira “haramtattun harkoki,” ita ce ta sanar da wannan takatarwar. Sanarwar ta ce takatarwar za ta fara aiki ne daga jibi Litini.
Hukumar ta kuma yi gargadi ga gidan rediyon Faransa (RFI), wadda ta zarga da bayar da rahotannin karya kan yiwuwar a yi bita-da-kulli ga masu kiran da a kada kiuri’ar rashin amincewa.
A wata takardar sanarwa ta jiya Jumma’a, Shugabar Gidan Rediyon VOA Amanda Bennet, ta yi tir da wannan mataki da Hukumar kula da yada labaran kasar Burundi ta dauka.