Kasar Brazil Ta Kaddamar Da Gangamin Rigakafin Cutar Zazabin Dengue

Your browser doesn’t support HTML5

Kasar Brazil ta kaddamar da gangamin rigakakin cutar zazabin dengue a daidai lokacin da kasar ta ke samun hauhawar kamuwa da cutar. A bisa bayanan ma’aikatar lafiyar kasar, Brazil ta samu hauhawar cutar da kusan ninki 5 cikin makonni 5 cikin wannan shekarar, wanda ya zarta na shekarar da ta gabata.