Kasar Pakistan ta kira jakadan Amurka a kasar domin ta nuna rashin amincewarta da sakon da shugaba Donald Trump ya sa a shafinsa na Twitter inda ya zargi kasar Pakistan da laifin baiwa ‘yan ta’adda dake fafatawa da sojojiin Amurka a Afghanistan dake makwabtaka da kasar mafaka.
Mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka a Islamabad ya ce, a jiya Litinin aka kira David Hale, zuwa ma’aikatar harkokin wajen kasar domin tattaunawa akan sakon da shugaba Trump ya aika ranar sabuwar shekara a shafinsa na Twitter.
Amurka ta dade tana zargin kasar Pakistan, musamman akan jami’an tsaronta, wajen yin kunnen kashi ko kuma taimakawa ayyukan kungiyoyin ta’addanci na ‘yan Taliban, da Haqqani dake kai hare-hare kan sojojin Afghanistan da Amurka ke yiwa jagoranci ta kan iyaka.
Islamabad ta musanta zargin taimakawa ‘yan ta’addan kasar Afghnaistan, a maimakon haka ta yi korafi kan yadda ‘yan gwagwarmaya ke amfani da makwabciyar ta wajen kai hare hare cikin Pakistan din.
A mayar da martani kan sakon Trump na twitter, ministan harkokin wajen kasar Pakistan Khawaja Asif, ya fada a ranar Litinin cewa “ kasar sa zata fadawa duniya banbamcin gaskiya da kuma kage."