Kasar Afghanistan Tace Sojojinta Zasu Iya Tsare Kasar

Gwamnatin Afghanistan ta nuna rashin damuwar ta game da rahoton dake cewa Amurka zata janye sojojinta daga kasar.

Gwanatin Afganistan na kokarin nuna rashin damuwa game da rahoton da ke cewa Amurka na shirin rage yawan sojojinta a kasar. Gwamnatin ta Afghanistan na cewa jami'an tsaron Afghanistan na iya kare kasar ba tare da taimakon kowa ba.

A cewar wasu jami’an gwamnatin Amurka a Washington, Shugaban Amurka Donald Trump na duba yiwuwar janye kusan rabin sojojin wadanda yawansu a Afghanistan ya kai kimanin 14,000.

Sojojin Amurka na cikin rukunin sojojin NATO 20,000 wadanda ba su shiga yaki, da asalin aikinsu shi ne koyar da dabarun yaki da kuma bayar da shawara ga sojojin Afghanistan a yakinsu da 'yan ta’adan kungiyar Taliban masu alaka da ISIS.