Karon Farko Gwamnatin Kamaru Ta Gana Da Shugabannin 'Yan Aware

Shugaban Kamaru Paul Biya

Wakilan gwamnatin Kamaru sun gana da manyan shugabannin ‘yan awaren kasar da ke yankin da ake magana da harshen Ingilishi a karon farko tun bayan barkewar rikicin yankin a shekarar 2017, a cewar wani shugaban ‘yan aware da kuma wasu jami’an tsaro guda biyu a ranar Juma’a 3 ga watan Yuli.

Julius Ayuk Tabe, madugun ‘yan awaren da aka fi sani wanda a yanzu ya ke daure a gidan yari bayan da aka yanke ma shi hukuncin daurin rai saboda wasu laifuka ciki har da ta’addanci, ya ce a ranar Alhamis 2 ga watan Yuli aka yi zaman don tattaunawa akan yiwuwar tsagaita wuta, a cewar Wani rahoto na kamfanin dillancin labaran Reuters.

Zanga-zanga kan rikicin Kamaru

A shekarar 2017 ne aka fara tashin hankalin biyo bayan wasu matakai da gwamnatin kasar ta dauka akan wasu lauyoyi da malaman makaranta da suka yi zanga-zangar lumana a yankin da ake magana da harshen Ingilishi don nuna rashin jin dadinsu akan yadda aka maida yankin saniyar ware.

Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 3,000 dubban mutane kuma suka gujewa matsugunnansu.