Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu girbe amfanin goma masu dinbin yawa, musamman ma dai Shinkafa wacce akasari itace babban abincin al’ummar kasar. A jihar Kebbi kadai an samar da Shinkafa fiye da ton Miliyan ‘daya da ake sasashe, a kadada fiye da Dubu 500 da aka noma a kananan hukumomi 10 a jihar.
Sai kuma wannan bai yi tasiri ba a wajen samun saukin farashin da wadatar abincin ga talaka, abin da wasu suka ta’allaka da yadda ake tsallakawa da abincin a domin sayarwa a makwabtan kasashe.
Malami a sashen nazarin tsimi da tattalin arziki na Jami’ar Usmanu dan Fodiyo ta Sokoto, Rufa’I Shehu, na ganin cewa sayar da abincin da ake nomawa a kasashen ketare bazai haifar da ‘da mai ido ba ga Najeriya.
A nasu bangaren manoma na ganin wannan lamari a zaman ci gaba a sha’anin aikin gona da a baya ya tabarbare. Mohammed Lawal Mai Doki, yace basa fatan ace abincin da suka noma baya fita zuwa wasu kasashe.
Yayin da gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta haramta tsallakawa da kayan abinci zuwa makwabtan kasashe. Takwaransa na jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, na ganin wannan bace matsalarba. Yana mai cewa idan farashin kayan abinci ya tashi mutane su kara nomawa, domin samarwa da wasu aikinyi.
A kwanannan ne dai mai taimakawa shugaban kasa a sha’anin watsa labari Mallam Garba Shehu, yayi gargadin cewa Najeriya kan iya fuskantar matsalar karancin abinci ya zuwa watan Janairun sabuwar shekara, sakamakon fita da ake yi da dinbin da ake nomawa domin sayarwa a makwabtan kasashe.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5