Adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 ya kai 43,537 a Najeriya a cewar hukumar NCDC mai sa ido akan cututtuka masu yaduwa a daren ranar Asabar 1 ga watan Agusta.
WASHINGTON, D.C —
A sakon da take sabuntawa a duk rana a shafinta na Twitter, hukumar NCDC ta ce an samu karin mutum 386 da suka kamu da cutar a ranar Asabar. Cikin mutum 43,537 da suka kamu da cutar, 20,087 sun warke yayin da wasu su 883 suka mutu.
Hukumar ta kuma ce an samu adadi mafi yawa a ranar daga birnin tarayya Abuja inda aka samu mutum 130 sai kuma jihar Legas da ke biye da mutum 65.
Sauran jihohin sun hada da Ondo inda aka samu mutum 37, 29 Osun, 23 Plateau, 15 Rivers, 14 Enugu, 12 Nasarawa, 11 Bayelsa, 11 Ebonyi, 9 Ekiti, 8 Oyo, 8 Edo, 6 Abia, 3 Ogun, 3 Katsina, 1 Imo, sai kuma 1 Adamawa.