Karin Bayani Kan Zarge-zargen Cin Zarafin 'Yan Najeriya a China

Fatimah Uwa Jibril

Tun bayan da duniya ta samu labarin cewa ana ta cin zarafin ‘yan Afurka, musamman ma ‘yan Najeriya a China, duniya ta yi ca ma wannan kasa. Tun sannan ‘yan jarida su ka shiga neman bayanan hakikanin abin da ya faru ko ya ke faruwa.

Cikin wadanda Muryar Amurka ta tuntuba a Chinar don jin abin da ya faru, har da wata dadaddiyar ‘yar jarida, Hajiya Fatimah Uwa Jibril, ta wani kamfanin sadarwa na Startimes Media mai hedikwata a birnin Beijing.

Hajiya Fatimah dai ta ce sharadinta na yin magana shi ne a yadda ta fadi gaskiya komai dacinta saboda ita ta fi so ta bugi jaki ta kuma buki taiki. Muryar Amurka kuwa ta ce ai haka ma tsarinta ya ke.

Muryar Amurka ta fara da tambayar Hajiya Fatimah yadda ta ke ganin wannan rigimar. Kamar sauran majiyoyi masu tushe, Fatimah ta alakanta rigimar da salon hukumomin China na dakile yaduwar cutar coronavirus, wanda ‘yan Afurka, musamman ma ‘yan Najeriya, ke ganin ana fakewa da shi a masu kwasar karar mahaukaciya a jibge su a wuraren killace su.

Saidai Hajiya Fatimah ta ce, ‘yan Najeriya ne su ka jawo ma kansu matsala. Ana killace su cikin mutunci kamar kowa, sai su ka shiga yin karan tsaye ma dokar zama a killace. Ta ce akwai ma wani dan Najeriya da ya raunata wata mai kula da masu dauke da cutar; baya ga haka kuma, wasu ‘yan Najeriya da aka killace a wasu otal-otal har raye-raye aka ce sun shiga yi. Wannan, a cewarta, shi ne mafarin daukar tsauraran matakai kan ‘yan Najeriya da ma duk wani dan asalin kasar ta Sin ko bako da ya bijire ma umurin zama a killace.

Da ta ke cigaba da amsa tambayoyin Muryar Amurka, Hajiya Fatimah ta ce baya ga kin bin umurnin zama a gida, dama ana zargin ‘yan Najeriya da yawan aikata wasu laifukan kuma. Ta ba da misalai iri-iri. To amma ta ce su ma ‘yan China ba salihai ba ne fa. Wasunsu na da raini da kuma taurin kai game da abin da ya shafi bukatar mutunta bako.

Ga kadan daga hirar Hajiya Fatimah Uwa Jibril da Ibrahim Ka-Almasih Garba:

Your browser doesn’t support HTML5

China Da 'Yan Najeriya: Kowa Da Laifinsa