A jahar Adamawa ta arewa maso gabashin Najeriya, wasu matafiya da kuma direbobi sun gudanar da zanga-zangar lumana tare da datse hanyar Mayo-Belwa zuwa Ganye, sakamakon cin zarafin da su ke zargin wasu sojoji sun yi wa wasu masu ababen hawa da suka hana su na goro.
Lamarin dai ya kawo tsaiko tare da hana zirga-zirga na tsawon wasu sa'o'i, yayin da yau ne ake cin babbar kasuwar kasashe ta Ganyen.
Matafiya da direbobin sun nuna fushinsu game da abun da suka kira cin zarafi da tatsar su da suke zargin wasu sojoji na yi akan hanyar zuwa garin Ganye da ke kudancin jihar Adamawan.
Cikin kwanakin nan ne dai aka bada umarnin janye shingayen da sojoji da sauran jami'an tsaro kan kafa da sunan duba ababen hawa, inda sau tari kan rikide ya zama tamkar wurin karbar haraji.
Ga dai wakilinmu a Adamawa Ibrahim Abdul'aziz da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5