Wani mazaunin garin Bajoga da ya tattauna da Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa ana ci gaba da jin karar harbe-harbe da fashe-fashe a yankin arewacin garin.
WASHINGTON, DC —
Wani mazaunin garin Bajoga da ya tattauna da Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa ana ci gaba da jin karar harbe-harbe da fashe-fashe a yankin arewacin garin, ta inda ofishin gunduma da kuma na yanki na rundunar 'yan sanda yake.
Malamin yace tun misalin karfe 7 na safiya 'yan bindigar suka shiga garin, a karo na biyu cikin 'yan watannin nan, amma babu bayani na takamammen inda suka kai ma hari.
Sai dai yace da ma an san cewa akwai sansanin 'yan Boko Haram a wasu 'yan kananan garuruwa da kauyuka da suke kusa da nan a tsallaken kogi, kuma har cikin garin su na shigowa sayen mai.
Ga bayanin tattaunawarsa da Sashen Hausa.