Karancin Mai A Jihohin Adamawa Da Taraba.

Karancin man fetur a Najeriya.

Yayinda jama'a suke kwana a layi a gidajen mai, yan bunburutu-watau blak maket suna holewa.

Matsalar karancin mai da ake fuskanta a arewacin Najeriya, abun yana kara ta'azzara a jihohin Adamawa da Taraba.

Yayinda masu ababan hawa suke kwana akan layi a gidajen mai, a bayan fage, ko a blak maket kamar yada aka sansu, masu sayar da mai a jarkoki suna cin karensu babu babbaka.

Jama'a suna zargin kungiyar dillan mai da ake kira IPMAN, a zaman wacce suke janyo matsalar, wadanda suka yi magana da wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz, sun ce, gidajen mai musamman a jihohin Adamawa da Taraba, suna da mai, amma sun gwammace su sayar da man a kasuwar bayan fage inda zasu ci kazamar riba.

Amma da yake kare kungiyar dillalan man fetur, shugabanta a shiyyoyin Adamawa da Taraba, Alhaji Abubakar A Butu, yace ko kusa ba laifinsu bane. Yace duk da cewa kamfanin NNPC ta kasa tana sayar musu da mai kan ka'ida, basa samun man akan lokaci. Na biyu kuma a inda suke dauko man, basa samunsa kan kayyadajjen farashi.

Yanzu ana sayen galan daya na man fetur kan Naira 1,200.00 a bayan fage a Yola.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

karancin Mai a Adamawa da Taraba